Lafzullah

Hausaca Tefsir Notlari — Ebubekir Mahmud Gumi — Yasin 36:2 – Nas 114:4

Author / source: Ebubekir Mahmud Gumi (ö. 1992, Mâlikî) — QuranEnc.com (v1.2.2) · KATMAN: mealin dipnot/tefsir katmani (meal metni ALINMADI)

Contents
  1. Yasin 36:2
  2. Yasin 36:7
  3. Yasin 36:13
  4. Yasin 36:26
  5. Yasin 36:28
  6. Yasin 36:50
  7. Yasin 36:58
  8. Yasin 36:66
  9. Saffat 37:2
  10. Saffat 37:101
  11. Saffat 37:112
  12. Saffat 37:164
  13. Saffat 37:175
  14. Sad 38:13
  15. Sad 38:15
  16. Sad 38:16
  17. Sad 38:20
  18. Sad 38:24
  19. Sad 38:31
  20. Sad 38:33
  21. Sad 38:34
  22. Sad 38:35
  23. Sad 38:36
  24. Sad 38:41
  25. Sad 38:88
  26. Zumar 39:10
  27. Zumar 39:18
  28. Zumar 39:67
  29. Gafir 40:15
  30. Gafir 40:83
  31. Fussilat 41:25
  32. Shura 42:3
  33. Shura 42:13
  34. Shura 42:14
  35. Shura 42:37
  36. Shura 42:39
  37. Shura 42:44
  38. Shura 42:50
  39. Shura 42:51
  40. Zukhruf 43:6
  41. Zukhruf 43:14
  42. Zukhruf 43:15
  43. Zukhruf 43:27
  44. Zukhruf 43:31
  45. Zukhruf 43:32
  46. Zukhruf 43:41
  47. Zukhruf 43:58
  48. Zukhruf 43:60
  49. Zukhruf 43:65
  50. Zukhruf 43:77
  51. Zukhruf 43:86
  52. Dukhan 44:14
  53. Dukhan 44:29
  54. Dukhan 44:33
  55. Dukhan 44:34
  56. Dukhan 44:59
  57. Jasiya 45:3
  58. Jasiya 45:14
  59. Jasiya 45:16
  60. Jasiya 45:23
  61. Jasiya 45:26
  62. Ahƙaf 46:13
  63. Ahƙaf 46:15
  64. Ahƙaf 46:21
  65. Ahƙaf 46:26
  66. Ahƙaf 46:29
  67. Muhammad 47:4
  68. Muhammad 47:7
  69. Muhammad 47:16
  70. Muhammad 47:17
  71. Muhammad 47:18
  72. Muhammad 47:19
  73. Muhammad 47:21
  74. Muhammad 47:22
  75. Muhammad 47:25
  76. Muhammad 47:33
  77. Muhammad 47:36
  78. Fathu 48:2
  79. Fathu 48:10
  80. Fathu 48:11
  81. Fathu 48:15
  82. Fathu 48:16
  83. Fathu 48:18
  84. Fathu 48:20
  85. Fathu 48:21
  86. Fathu 48:24
  87. Fathu 48:26
  88. Fathu 48:29
  89. Hujurat 49:1
  90. Hujurat 49:2
  91. Hujurat 49:6
  92. Hujurat 49:9
  93. Hujurat 49:13
  94. Ƙaf 50:12
  95. Ƙaf 50:14
  96. Ƙaf 50:23
  97. Ƙaf 50:27
  98. Ƙaf 50:30
  99. Ƙaf 50:33
  100. Ƙaf 50:34
  101. Ƙaf 50:36
  102. Ƙaf 50:39
  103. Ƙaf 50:41
  104. Ƙaf 50:45
  105. Zariyat 51:57
  106. Tur 52:21
  107. Tur 52:39
  108. Tur 52:48
  109. Najm 53:5
  110. Najm 53:13
  111. Najm 53:17
  112. Najm 53:18
  113. Najm 53:19
  114. Najm 53:23
  115. Najm 53:32
  116. Najm 53:49
  117. Najm 53:53
  118. Najm 53:55
  119. Najm 53:57
  120. Najm 53:59
  121. Najm 53:62
  122. Ƙamar 54:1
  123. Ƙamar 54:27
  124. Ƙamar 54:45
  125. Rahman 55:13
  126. Rahman 55:26
  127. Rahman 55:31
  128. Waƙi'a 56:8
  129. Waƙi'a 56:13
  130. Waƙi'a 56:60
  131. Waƙi'a 56:87
  132. Waƙi'a 56:96
  133. Hadid 57:8
  134. Hadid 57:10
  135. Hadid 57:16
  136. Hadid 57:17
  137. Hadid 57:25
  138. Hadid 57:27
  139. Hadid 57:28
  140. Hadid 57:29
  141. Mujadala 58:1
  142. Mujadala 58:7
  143. Mujadala 58:11
  144. Mujadala 58:12
  145. Mujadala 58:14
  146. Mujadala 58:22
  147. Hashr 59:2
  148. Hashr 59:7
  149. Hashr 59:9
  150. Hashr 59:11
  151. Hashr 59:15
  152. Hashr 59:18
  153. Mumtahana 60:1
  154. Mumtahana 60:3
  155. Mumtahana 60:12
  156. Mumtahana 60:13
  157. Jumu'a 62:2
  158. Jumu'a 62:3
  159. Jumu'a 62:5
  160. Jumu'a 62:6
  161. Jumu'a 62:9
  162. Munafiƙun 63:1
  163. Munafiƙun 63:4
  164. Munafiƙun 63:8
  165. Tagabun 64:14
  166. Tagabun 64:15
  167. Talaƙ 65:1
  168. Talaƙ 65:4
  169. Talaƙ 65:6
  170. Talaƙ 65:8
  171. Talaƙ 65:11
  172. Tahrim 66:1
  173. Tahrim 66:2
  174. Tahrim 66:6
  175. Tahrim 66:7
  176. Tahrim 66:8
  177. Tahrim 66:10
  178. Tahrim 66:11
  179. Tahrim 66:12
  180. Mulk 67:30
  181. Ƙalam 68:33
  182. Jinn 72:16
  183. Jinn 72:19
  184. Jinn 72:27
  185. Muzzammil 73:15
  186. Ƙiyama 75:1
  187. Ƙiyama 75:2
  188. Ƙiyama 75:16
  189. Ƙiyama 75:30
  190. Ƙiyama 75:40
  191. Insan 76:13
  192. Mursalat 77:4
  193. Mursalat 77:13
  194. Nazi'at 79:20
  195. Abasa 80:1
  196. Takwir 81:4
  197. Takwir 81:7
  198. Takwir 81:8
  199. Takwir 81:15
  200. Takwir 81:23
  201. Takwir 81:24
  202. Mutaffifin 83:3
  203. Mutaffifin 83:21
  204. Mutaffifin 83:36
  205. Buruj 85:2
  206. Buruj 85:3
  207. Buruj 85:4
  208. Tariƙ 86:3
  209. Tariƙ 86:12
  210. Tariƙ 86:13
  211. Tariƙ 86:14
  212. A'ala 87:15
  213. A'ala 87:16
  214. A'ala 87:18
  215. Gashiya 88:15
  216. Fajr 89:7
  217. Fajr 89:9
  218. Balad 90:1
  219. Balad 90:6
  220. Balad 90:10
  221. Balad 90:18
  222. Balad 90:19
  223. Shams 91:9
  224. Shams 91:10
  225. Laili 92:6
  226. Laili 92:17
  227. Duha 93:4
  228. Tini 95:1
  229. Tini 95:2
  230. Tini 95:3
  231. Tini 95:8
  232. Alaƙ 96:19
  233. Bayyina 98:2
  234. Asr 103:1
  235. Fil 105:1
  236. Kafirun 109:5
  237. Masad 111:4
  238. Nas 114:4

Yasin 36:2

[1] Al-ƙur'ãni ma'anarsa abin karãtu.

Yasin 36:7

[1] Kalma a nan ita ce faɗar Allah da take cewa zai yi azãba ga kãfirin da bai yi ĩmãni ba.

Yasin 36:13

[1] Su Manzannin Ĩsã ne zuwa Antãkiya, bãbban garin kasar Rũmu. Sũ ne Yõhana da Pulis. Na uku, shĩ ne sham'ũn. Mutumin da ya jħ yanã gaggawa, shi ne Habĩb Masassaki wanda ya fãra gamuwa da Manzannin farko, ya yi ĩmãni da su, sa'an ya jħ yanã wa'azi ga mutãnensa.

Yasin 36:26

[1] An ce masa haka a bayan mutãne sun kashe shi sabõda ĩmãninsa. Wannan shi ne sakamakon mai wa'azi idan ya yi shahada a kan aikinsa na wa'azi.

Yasin 36:28

[1] Wãtau halakar da su abu ne mai sauƙi a gare Mu, ba Mu yi bukãtar saukar da wasu sõjõjin malã'iku daga samã ba.

Yasin 36:50

[1] Mãsu izgili ga addini idan ajali ya je musu bisa ga abke, bã zã a bã su dãmar wasiyya ba ga iyãlansu.

Yasin 36:58

[1] Ana ce musu aminci ya tabbata a gare ku, da magana daga wajen Ubangijinsu Mai rahama, watau ana fada musu haka da magana bã da wata ishãra ba.

Yasin 36:66

[1] Dã Mun so shãfe ganinsu na ido kamar yadda Muka shãfe basĩrarsu ta hankali, dã Mun shãfe shi, sai su zama makãfin idãnu kamar yadda suke makãfin zũci. Sabõda haka ko sun so gani, bã zã su yi ba.

Saffat 37:2

[1] Mãsu tsãwa, sũ ne Malamai mãsu sãmun ilmin wa'azi daga Annabãwa waɗanda ke karãtun abin tunãwa daga Allah Ubangijin sammai da ƙasa, Mai bãyar da haske ga rãnã, Mai haskaka taurari mãsu ƙãwãtar da samã kuma su tsare ta daga shaiɗanu. An siffanta rãnã da Annabãwa, Malamai da taurãri, ilmi da haske da sababin ƙawa da shiryarwa da kõrar mãsu ɓarna.

Saffat 37:101

[1] Yãron da aka yi bushãra da shi a nan, shĩ ne Ismã'ĩla' sabõda abin da yake tafe a gaba wanda ya shãfi Is'hãƙa da sũnansa a bayyane yã nũna a nan bã shi ba ne. Watau Ismã'ĩla kawai ne.

Saffat 37:112

[1] Wannan sãbuwar bushãra da Is'hãƙa tanã nũna cewa bã shĩ ne wanda kissar yankã ta shãfa ba sabõda haka Isma'ĩla dai ne tabbas, mai ƙissar yankã. Sabõda haka Allah Ya sanya shi wata al'umma dabam' dõmin a sãka masa, sa'an nan aka sãkawa Ibrãhĩm da Is'hãƙa dõmin ya zama wata al'umma ta dabam,.

Saffat 37:164

[1] Malã'iku da sauran halitta duka kõwa yã san matsayinsa na bauta ga Allah wanda ba Ya da dã ko diya, kuma ba Ya da dangantaka da kõwa.

Saffat 37:175

[1] Wannan ƙãrin bayãni ne ga abin da sũrar ke karantarwa na cewa Annabãwa sũ ne kamar rãna mai haske na asali. Mãlamai kamar taurãri suke mãsu sãmun haske daga rana su wãtsa ga dũniya kuma su kõre ɓarna. Aya ta l79 da ke tafe karfafawa ce ga ma'anar wannan.

Sad 38:13

[1] Mutãnen ƙunci, sũ ne mutãnen Annabi Shu'aibu. A cikin Sham suke.

Sad 38:15

[1] Watau mutãnen Annabi Muhammadu: Ƙuraishãwa da waninsu har ya zuwa Tashin Ƙiyãma.

Sad 38:16

[1] Wannan ita ce maganar dukan kãfirai na kõwane zãmani mãsu nħman rabon dũniya kawai, ba su yarda da Tãshin Ƙiyãma ba, balle sãmun sakamako a cikinsa.

Sad 38:20

[1] Hikima, ita ce Annabci, rarrabe magana, shĩ ne sanin hanyar yin sharĩ'a da rarrabe mai ƙãra daga wanda aka yi ƙãra, da neman shaidu daga mai ƙãra da neman rantsuwa ga mai musu.

Sad 38:24

[1] Dãwũda ya yi hukunci da zãlunci ga wanda ya yi ƙãra, sabõda abin da ya rufe shi na ƙin zãluntar mai rauni wanda Allah Ya hana. Nauyin wani laifi ya rufe shi daga tunãwa da wani laifi, watau yin hukunci tun binciken shari'a bai cika ba, sabõda iya maganar wani abõkin ƙãra. Wannan shĩ ne fitinar da ta same shi kawai kuma a kanta ya yi nadãma, kuma a kanta ne Allah Ya yi masa gargaɗin kada ya bi son rai mai sanya Fushi kõ yarda ga abin da bai cancanci haka ba. Yarda da wata ƙissar mãtar Uriya wadda Yahũdãwa ke sanyãwa, a nan, kãfirci ne ga Musulmi, dõmin ta kõre ismar Annabãwa, kuma ba ta dãce da lafazin Alƙur'ãni ba.

Sad 38:31

[1] Shĩ ne dõki mai tsayuwa a kan ƙafãfu uku. Wannan yanã nũna asalinsa mai kyau ne.

Sad 38:33

[1] Sulaimãna ya yanka dawãkin,dõmin kallonsu yã hana shi salla, wadda take farlu ainin ce a gare shi, amma tattalin kãyan yãƙi farlu kifãya ce. Anã gabãtar da farlu ainin a kan farlu kifãya. Wannan kuma ya nũna cewa anã cin dõki idan wani dalĩli bai hana ba. Dũbi Sũra ta 16, ãyã ta 8.

Sad 38:34

[1] Wata rãna Sulaiman ya yi tunãnin ya sãdu da mãtansa ɗari uku, dõmin su yi cikunna su haifi diya mãsu taimakonsa jihãdi fi sabilillahi, amma ya manta, bai ce in Allah Yã so ba. Sai ya sãdu da su, ba su yi cikin ba, sai guda ɗaya daga cikinsu, kuma ta haife shi bãbu rai. Ma'anar kissar, ita ce ko aikin Allah, sai mutum ya mayar da yinsa ga mashĩ'ar Allah, sa'an nan zai ci nasara a kansa.

Sad 38:35

[1] Yã yi wannan addu'a dõmin kada wani ya yi alfahari da sarauta a bãyansa, ya halaka kuma ya halakar da wani. Sarauta ita ce asalin girman kai da alfahari. Bã ka ganin wanda ya shiga wajan sarki, dõmin ya gaishe shi, idan ya fito daga gare shi, sai ya ɗõra yin tãƙama dõmin abin da zuciyarsa ta ɗebo daga girman kan sarkin da alfaharinsa?.

Sad 38:36

[1] An hore masa iska matsayin dawãkin da ya yanke dõmin Allah. An hõre masa aljannu dõmin niyyarsa ta sãmun diya mãsu jihãdi dõmin Allah.

Sad 38:41

[1] Wannan ƙissa tanã nũna haƙuri ga riƙon iyãli, mulkin ƙasã da mulkin gida duka daidai suke, sai yadda Allah Ya yi umurni a yĩ su. Haka mallakar rai idan mutum bai bi umurnin Allah ba a cikinsu, sai su buwãye shi tsarewa, kamar yadda mulkin ƙasa ke buwãya a riƙe shi tãre da kãfirci da zãlunci.

Sad 38:88

[1] Bauta wa gumãka da hidimar shehunai da suka mutu waɗanda suka shirya wani sãbon abu da bãbu ga sunnar Annabi duka ɗaya suke, dõmin kõwanensu kiran wanin Allah ne sabõda neman ãgaji.

Zumar 39:10

[1] Bãbu dalĩli da zai sanya mutum ya zauna a inda bã ya iya bautawa Ubangijinsa da kyau. Watau hijira zuwa wurin yardar Allah, wãjibi ne, sai idan dũniya ta zama haka a kõ'ina bãbu wurin tafiya, kõ kuma tafiya can da wuya ƙwarai tanã kallafa nauyin da zai zama wani laifin da ke daidai da rashin hijirar, to, sai mutum ya zauna, ya tsare kansa gwargwadon hãli.

Zumar 39:18

[1] Bãyin Allah na ƙwarai sũ ne waɗanda suke saurãren maganar Allah, sa'an nan su yi aiki da abin da yake mai bayyanannar ma'ana daga gare ta, kuma su bar abin da ba su gãne ma'anarsa ba bãyan sun yi ĩmãni da shi cewa daga Allah yake, kuma su tsarkake Allah daga abin da ba ya sifantuwa da Shi na sũrõrin hãlittarSa.

Zumar 39:67

[1] Yã yi bayãnin yadda zã a iya ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin ĩkon yin Sa da cewa, "ƙasã duka damƙarSa ce har zuwa ƙarshen sũrar. Wãtau yã dunƙule sũrar abũbuwan da zã su auku a Rãnar Ƙiyãma dõmin su bai wa mai hankali yadda suranta ikon yi na Allah Mai girma zai yiwu.

Gafir 40:15

[1] Rũhi a nan, ga fahimta ta, Allah ne Mafi sani, shĩ ne karfin rai da basĩrar fahimtar addĩni da aiki wajen rãyar da shi, wanda Allah Yake sakãwa ga mãlamin da Yake nufin jaddada addini da shi a kan kõwane karni kamar yadda Hadisi ya zo da shi, ya kõre jidãlin mãsu jidãli.

Gafir 40:83

[1] Ilmin dũniya na sanã'õ'i ya zõ ne daga Annabãwa kamar na ibãdu. Nũhu ya fãra sassaƙar jirgin ruwa da wahayi daga Allah, Zulƙarnaini ya fãra haɗa baƙin ƙarfe da gaci dõmin hana tsãtsa, Yũsufu ya fãra barin hatsi a cikin sõshiya dõmin hana ƙwãri. Dãwũda ya fãra sanã'ar sulke. Ãdam ya fara rubũtu, Idirĩsu ya fara yin alƙalami. ĩsã ya fãra warkar da majinyata, Alƙur' ãni ya nũna anã iya tãshi sama da jirgin sama. Shu'aibu shi ya nũna kasuwanci, da sauransu.

Fussilat 41:25

[1] Mabiya, sũ ne aljannun kõ Shaiɗãnun da ke tãre da mutum.

Shura 42:3

[1] Asirin haɗa jama'a bã zã su rarrabu ba. Watau su riƙi Allah Shi kaɗai ne Ubangiji Mai yin umurni ko hani, kuma su riƙi cewa Muhammadu, tsĩra da aminci su tabbata a gareshi, shĩ ne cikamakin Annabãwa, bãyansa bã a bai wa kõwa kõme fãce fahimta ga abin da ya zo da shi.

Shura 42:13

[1] Ku bi umurnin Allah kamar yadda Ya aza muku hukunce-hukuncenSa, kada ku karkace da bin umurnin waɗansu na dabam waɗanda bã Allah ba, kõ kuma kada ku bi son zũciyarku. Bin umurnin wani zai sanya ku sãɓãwa jũnanku, ku rarrabu, ku rasa ƙarfi a kan maƙiyanku. Wanda ya bi umurnin waɗansu, waɗanda bã Allah ba, to ya yi shirka da Allah ke nan kuma haɗuwar mãsu bin umurnin waɗansu waɗanda bã Allah ba, to, tanã da wuya. Wannan ãya ta hana bin ɗarĩƙõƙin ƙungiyõyin sũfãye duka, dõmin bin su, bin umurnin waɗansu ne waɗanda bã Allah ba kuma yanã rarraba Musulmi, su zama ƙungiya-ƙungiya, da sãɓãni mai nĩsa. Bã zã a ce ba, "Ã'aha! Wannan ãya ta sauka ga Yahũdu da Nasãra kawai" dõmin ãyõyi biyu l4 da l5, mãsu bin wannan, sun gama harda Musulmi, dõmin umurni ga Annabi, umarni ne sabõda al'ummarsa. Kuma sãɓãnin mãsu ɗariƙõƙi sãɓãni ne a kan asali watau aƙida, bã sãɓãnine a kan rassuna na furũ'a ba. Sabõda haka bãbu ƙiyayya a tsakãnin mabiya mazhabõbi, dõmin sãɓãninsu, na fahimta ne kawai. Sãɓãni ga reshe, rahama ce, amma sãɓãni ga asali azãba ce. [2] Watau haɗuwar jama'a ga bin addini guda, bã da sãɓawa ba ga asalinsa. Wanda ya ce: An saukar wa wani mutum, baicin Muhammadu, da wani abu daga Allah, to, shĩ ya sãɓãwa asali. Sãɓãwa ga asali kãfirci ne.

Shura 42:14

[1] Kalmar da ta gabãta, ita ce "Allah bã zai halaka mutane ba sabõda zunubi sai ajalinsu ya zo." Zãlunci da ke hana su haɗuwa a bãyan sanin gaskiya, shi ne hassadar jũna, sa kwaɗayi da son shugabanci a cikin mu'amala.

Shura 42:37

[1] Bayãnin siffõfin mũminai, waɗanda suke tsare su, Yana lãmunce zama haɗe, da gamuwar Musulmi, sũ ne siffõfi shida, nisantar manyan zunubbai da zina, da gãfarta fushi, da tsayar da salla, da shãwara ga al'amuran tsakãninsu, da ciyar da dũkiya da ta wajabci mutum ya ciyar da ita a cikin alheri ga inda Allah Ya ce a ciyar da ita.

Shura 42:39

[1] Wajen rãma zãlunci kõ yinsa, mutãne sun kasu kashi huɗu. Mãsu rãmãwa gwargwadon zãlunci, bã su da laifi; da mãsu rãmãwa da abin da ya fi laifin da aka yi musu, to, sunã da laifi kamar mãsu fãra zãlunci, da mãsu gãfartãwa, waɗannan sũ ne Allah ke so.

Shura 42:44

[1] Bayãnin mai zãlunci da sakamakonsa a Rãnar Lãhira.

Shura 42:50

[1] Bakarãrre, shi ne wanda bã ya haihuwa.

Shura 42:51

[1] Annabãwa a lõkacin da Allah Ya yi musu magana ba su gan shi ba, sai dai sun ji maganarsa kamar yadda Musã ya ji, kõ kuma da wãsiɗar malã'ika kamar sauran Annabãwa, kõ kuwa da ilhama watau ya san hukunci ba da magana kõ wani wãsiɗar malã'ika ba. Ilhãmar Annabãwa da mafarkinsu gaskiya ne. Ilhãma da mafarkin sauran mutãne bã ya zama hujja sai idan yã dãce da shari'a, sai a yi aiki da shi a kan shari'a bã a kan mafarkin ko ilhãmar ba.

Zukhruf 43:6

[1] Tun da ba Mu bar mutãnen farko mãsu ɓarna ba, sai da Muka aika musu Manzanni, kuma kõwace ƙungiya daga cikin waɗanda aka aikawa wani Manzo sai da ta yi izgili game da Manzonsu, har abin ya kai ga halakar shũgabanninsu. To, haka mutãnenka, bã zã Mu bar su ba, sabõda ɓarnarsu, sai Mun aike ka zuwa gare su, su yi izgili game da kai, har a halaka shũgabanninsu, sa'an nan sauransu, su bi abin da aka umurce su da shi.

Zukhruf 43:14

[1] Ku yi dalĩli da hõrewar abin hawa gare ku zuwa ga tabbatar tãshinku dõmin hisãbin Ƙiyãma, dõmin ku bi umurninsa a dũniya, kuma ku bar al'adunku.

Zukhruf 43:15

[1] suka ce malã'iku 'ya'ya mãtane na Allah, sunã bauta musu ne dõmin su kusantar da su zuwa ga Allah, watau dõmin su cece su daga azãba. Sun yi wannan ƙarya ne dõmin su tabbatar da al'ãdarsu ta surkulle. Sabõda haka suka yi wa Allah ƙarya suka naƙasa shi da haka, kuma suka naƙasa malã'iku mãsu daraja a wurin Allah kuma suka kãfirce wa ni'imar da Allah Ya yi musu wajen aiko musu Manzo mai shiryar da su. Sa'an suka kafa hujja da ƙarya dõmin su danne gaskiya.

Zukhruf 43:27

[1] Bã ni bauta wa gumãka, amma inã bautawa Allah wanda Ya ƙãgi halittata.

Zukhruf 43:31

[1] Sunã nufin Makka da tã'ifa, kuma sunã nufi a saukar da Alƙur'ãni ga walĩdu ɗan Mugĩra na Makka kõ ga Urwatu ɗan Mas'ũdi As saƙafi a Ta'ifa. Watau sunã sũkar Muhammadu dõmin bã shi da dũkiya. A gare su mai dũkiya shĩ ne babban mutum, wanda ya cancanta Allah Ya aiko shi ga mutãne.

Zukhruf 43:32

[1] Tun da ba Mu bar rabon abincin rãyuwarsu ta dũniya a hannunsu ba, to, ta yãya ne zã Mu bar babban abu kamar Annabci da shiryar da mutãne ga hannãyensu? Wãtau bã zai yiwu Mu yi ba sai yadda Muke so kawai, kõ su bi, kõ su kãfirta, duka daidai ne a gare Mu.

Zukhruf 43:41

[1] Mu tafi da kai, watau Mu karɓi ranka, ka mutu, to, dã Mun yi musu azãba ke nan, dõmin sun rasa mai shiryar da su.

Zukhruf 43:58

[1] Wãtau da aka ce gumãka damãsu bauta musu duka abincin wutar Jahannama ne kamar yadda yake a cikin sura ta 21 ãyã ta 98 da 99, sai suka ce sun yarda gumakansu su zama tãre da ɗan Maryama.

Zukhruf 43:60

[1] Dã Mun so dã Mun sanya ɗiyansu su zama malã'iku, su fi Ĩsa ɗan Maryama zama abin mãmãki ga halitta, sa'an nan su maye muku a cikin ƙasã maimakon ɗiya masu siffõfi irin na jikunkunanku. Zai fi zama abin mãmãki mutum yahaifi malã'ika bisa mace ta haifi ɗã bã da wani namiji yã kusance ta ba.

Zukhruf 43:65

[1] Nasãra suka kasu a cikin ƙungiyõyi a bayan Ĩsã. Ya'akubiyya, mãsu cewa Ĩsã ɗan Allah ne, da Malakãniyya, mãsu cewa Ĩsa ɗayan uku ne. Waɗansu kuma suka ce bãwan Allah ne watau su ne Musulminsu, kuma waɗansu daga Musulmin suka kãfirta a bãyan zakuwar, Muhammadu tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, sabõda sun ƙi yarda da Annabcinsa. Yahũdu suka ce: "Ĩsã bã Annabi ba ne dan zina ne." Allah Ya la'ani kãfirai dukansu.

Zukhruf 43:77

[1] Watau sunã neman su mutu su huta da ɗaukar aZãba.

Zukhruf 43:86

[1] Su waɗanda suka yi shaida da gaskiya sun san bãbu mai mallakar ceto ga wani fãce Allah. Sabõda haka Allah nã yi musu izni su ceci wanda Yake son su cece shi, ba wanda su suke so ba. Ma'anar iznin da ceto ga bãyin Allah sãlihai ita ce dõmin Allah Ya bayyana darajar mai ceton ne kawai, bã don yanã da wani hakki ba, ga Allah. Allah Ya tsarkaka daga wata halittar Sa ta sãmi wani hakki a kan Sa. Kõwa bãwan Sa ne.

Dukhan 44:14

[1] Sunã nufin waɗansu mutãne ne ke gaya wa Annabi Alƙur'ãni, kõ kuma daga alãma watau wai Annabi taɓaɓɓe ne, mahaukaci. Taɓaɓɓe da mahaukaci duka ma'anarsu guda ce, watau marashin hankali,wanda aka yi wa alãma da rashin hankali.

Dukhan 44:29

[1] Watau sama da ƙasa ba su girgizu ba sabõda halaka su da aka yi kamar ba a yi, kõme ba.

Dukhan 44:33

[1] An bai wa Banĩ lsrã'ĩla ni'imar ilmi na Taurãta, an ɗaukaka su, sabõda aiki da ilmin, a kan sauran mutãnen zãmaninsu, kuma aka bã su ãyõyin mu'ujiza kamar tsãge teku da mannu da salwa da sauransu, amma kuma dukkan waɗannan ni'imomĩn sai da suka gushe a lõkacin da suka sãɓawa umurnin Allah, sai kuma ƙasƙanci ya maye musu daga bãya. Wannan kuma wa'azi ne ga Musulmi waɗanda Allah Ya ɗaukaka su da Alƙur'ãni a kan sauran mutãne, idan sun kauce masa zã su wulãkantu.

Dukhan 44:34

[1] Anã nufin mutãnen zãmanin Annabi Muhammadu, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, waɗanda ake kiran su zuwa ga Musulunci.

Dukhan 44:59

[1] Mãsu jira ne ga abin da zai sãme su idan ba su yi ĩmãni ba, watau ni'imar da aka ba su zã ta gushe ke nan dõmin ba su aiwatar da ita ba a kan umuruin Allah.

Jasiya 45:3

[1] Ãya, ita ce alãma mai jan hankalin mutum zuwa ga shiriya. Jam'inta, shi ne ãyõyi.

Jasiya 45:14

[1] Kwanukan Allah, sũ ne masĩfu waɗanda ke sãmun kãfirai waɗanda bã su bin sharĩ'ar Allah. Wãtau Allah Ya umurci Annabi ya gaya wa Musulmi, cewa wanda bã ya tsõron masĩfu sabõda ya ki aiwatar da sharĩ'ar Allah a kansa to kada Musulmi su dãmu da shi, watau kãfiran amãna nã iya bin dõkõkinsu na al'ãda, bãbu ruwan Musulmi matuƙar dai ba su shũka wata fitina ba a gare su. A bãyan haka Allah zai sãka wa kõwa game da aikinsa.

Jasiya 45:16

[1] Bã Musulmi kawai aka aikowa Manzo ba,ba su kawai aka bã su sharĩ'a ba, kuma aka umurce su da binta ba, Banĩ Isrã'ĩla ma an bã su haka kuma sunɗaukaka a kan mutãne a lõkacin da suka yi aiki da sharĩ'ar, kuma suka ƙasƙanta a lõkacin da suka bar aiki da ita. Musulmi ma haka suke idan sun bar sharĩ'ar da Allah Ya aza su a kanta, zã su ƙasƙanta yadda Yahũdawa suka ƙasƙanta.

Jasiya 45:23

[1] Ilmin Allah bã shi da iyãka, Yanã bũɗa shi ga wanda Ya ga dãma, a inda kõ a lõkacin da Ya ga dãma, amma dai duk ilmin da bai saukar da shi ga Annabi Muhammadu ba, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, to, bã a aiki da shi ga hukunci kõ sharĩ'a, wanda ya bi shi kuwa, to, ya ɓace ga aikinsa, bã ya cikin shiryayyu mãsu zaman lãfiya a dũniya kuma su shiga Aljanna a Lãhira, dõmin sharaɗin haka shĩne bin sunna. Wanda ya bar sunna kuwa, ya yi kuskuren hanya, bãbu mai shiryar da shi kuma sai Allah idan Yã so shi da rahama, watau Ya sanya shi ya tũba. Wannan ya nũna cewa ibãda da mu'ãmala duka ɗaya suke ga Musulunci, barin aiki da sharĩ'a a cikin kõwannensu duka, kãfirci ne ga wanda ya halatta yin haka nan. Mafi yawan kãfircin da ya sãmi Musulmi, ya zo musu ne ta hanyar barin mu'ãmalõli da sharĩ'ar Allah, suka ɗauki yin salla da mai kama da ita, shi kaɗai ne Musulunci, suka kãfirta da haka.

Jasiya 45:26

[1] Wãtau ba kũ ne ke rãyuwa da kanku ba, sai an rãyar da ku, haka ne ga mutuwa, bã ku ne ke mutuwa da kanku ba, sai an matar da ku, kuma Allah Shi Ɗaya ke iya rãyarwa ko matarwa. To, yãya ne zã ku ƙi bin sharĩ'ar da Ya umurce ku da binta?.

Ahƙaf 46:13

[1] Yã fara da wanda ya yi wa kansa nasĩha, kuma ya yi aiki da ita, to, shĩ mai gargaɗi ne. Haka kuma mai yin nasĩha ga mutãne, shĩ mã mai gargaɗi ne.

Ahƙaf 46:15

[1] Mutum a cikin iyãlinsa, kõ ya zama mai gargaɗi ga kansa da nasĩha ga mahaifansa da zuriyarsa kamar yadda ya bayyana a cikin ãyõyi 13,l4 da l5, kõ kuma ya zama mai butulci ga kansa, ya tõzartar da iyãyensa da zuriyarsa, kamar yadda ya bayyanaa cikin ãyõyi 17 da 18.

Ahƙaf 46:21

[1] Ya ambaci hũdu da mutãnensa Ãdãwa da misãlin waɗansu mãsu garagaɗi daga Annabãwan da suka shũɗe da kuma mutãnensu da yadda aka halaka su daga inda suke zaton rahama ta Je musu. Haka ne hukuncin. Dukan wanda aka yi wa gargaɗi da bin umurnin Allah, idan ya ƙi bi, sa'an nan ya bi son zũciyarsa, Allah zai Kãwo masa azãba daga inda yake zaton alheri ga kansa.

Ahƙaf 46:26

[1] Ya wajaba a gare su, watau sakamakonsa ya tabbata a kansu da azãba.

Ahƙaf 46:29

[1] Wannan yã nũna cewa a cikin aljannu akwai Musulmi da masu gargaɗi, kuma idan mutum ya yi gargaɗi, dõmin Allah, Allah zai taimake shi da mãsu saurãra masa, kõ da daga waɗansu jinsin da ba nãsa ba. Kuma zama a cikin wani addinin Allah da ya shige, ba ya isa ga wanda bai shiga addinin Musulunci ba, a bãyan bayyanar Musulunci.

Muhammad 47:4

[1] Tafarkin Allah, (fi sabilillahi)a wannan sũra tanã nufin jihãdi na takõbi dõmin ɗaukaka kalmar Allah da tsare ta. Anã fassara tafarkin Allah a waɗansu wurãre da jihãdi na takõbi kõ na magana dõmin shiryar da mutãne kõ dõmin tsaron gaskiya, kõ kuma karantarwa, da kuma tsare rai daga sha'awarta da fushinta. A cikin Hadisi anã ruwaitõwa cewa tsaron rai daga sha'awarta da fushinta shĩ ne jihãdi wanda ya fi girma.

Muhammad 47:7

[1] Tabbatar da dugadugan ƙafãfun, yanã nufin sanya musu jãrumta a cikin zukãtansu, dõmin ƙafãfunsu, su kafu a wurin yaƙi, dõmin kada su gudu.

Muhammad 47:16

[1] Wannan shĩ ya nũna cewa wani ɗan rahõto ba zai iya fahimtar gaskiya ba, matuƙar anã aikin Allah da gaskiya. Allah na sanya tsõro a cikin zukãtan kãfirai.

Muhammad 47:17

[1] Taƙawa, ita ce bin umarnin Allah da nĩsantar haninsa sabõda haka abin da Allah ke bai wa mai taƙawa, shi ne sakamkon aikinsa wanda ya yi daidai da sunnar Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare Shi.

Muhammad 47:18

[1] Tunãwarsu da wa'aztuwarsu ga Sa'a bã zai yi musu amfãni ba, a bãyan tã je musu. Wa'azi bã ya amfãni, sai idan wanda aka yi wa shi, yã yi aiki da shi a gabãnin mutuwa ta je masa.

Muhammad 47:19

[1] An umurci Annabi ya nemi gãfara dõmin mutãne su yi kõyi da shi, dõmin Allah Ya riga ya tsare shi daga zunubi a gabãni da bayan Manzanci.

Muhammad 47:21

[1] kulluwar a'lamari, shĩ ne umurni da yin yãƙi, yi wa Allah gaskiya, shĩ ne zartar da umurninSa, bã tãre da tsõro ba. Tsõro mũnafunci ne.

Muhammad 47:22

[1] Dõmin barin jihãdi yanã kai ga wãtsuwar ɓarna da fasãdi a cikin ƙasã. Wãtsuwar fasãdi,yanã kai ga yanke zumunta tsakãnin dangi, sabõda zãluntar jũna.

Muhammad 47:25

[1] Barin jihãdi, ridda ne da kõmãwa zuwa ga kãfirci da ƙawãtãwar Shaiɗan cewa rashin zuwa yãƙi na sanya kwanciyar hankali da rashin mutuwa, kuma yanã sanya musu waswasi da haka.

Muhammad 47:33

[1] Kada ku ɓata ayyukanku da ƙin ɗa'a ga Allah da Manzon Sa ga fita zuwa yãƙi da waninsa. Ridda na ɓãta ayyuka, kuma riya da mãmãkin kai na ɓãta lãdar ayyuka, kuma ƙwãra da cũtarwa sunã ɓãta lãdar sadaka. Sauran manyan zunubbai, bã su ɓãta ayyuka sai ga ra'ayin Mu'utazilãwa mãsu cewa manyan zunubbai na ɓãta lãdar ayyuka kamar ridda. An ɓãta maganarsu da ãyar da ke cewa: "Allah na gãfarta abin da ya kãsa hãka ga wanda Yã so." Sũratun Nisa'i ãyã ta48.

Muhammad 47:36

[1] Wãsã, shi ne dukan aiki wanda aka yi bã da nufin wata fa'ida ta addini ba, watau anã yin sa ne dõmin a sãmi abin aikatãwa a ɓãta lõkaci. Dukan ayyukan da mutum ya yi da nufin rãyuwar dũniya kawai, to, ya zama wãsã kõ dã cin abinci ne da karãtu. Kuma duk abin da mutum ya yi da niyyar bin umurnin Allah, wãjibi to ya zama aikin Lãhira kõ da cin abinci ne da jima'insa da matarsa, kamar yadda yake a cikin Hadĩsin Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Fathu 48:2

[1] Laifin Annabi wanda Allah Ya gãfarta, shĩ ne a lõkacin da ya fãra kiran mutãne zuwa ga bauta wa Allah, Shĩ kaɗai, mãsu bauta wa waɗansu abũbuwa sun ga laifinsa a wannan, sun yi ƙiyayya da shi sabõda haka, har suka yi yãƙi da shi, dõmin tsare ibãdarsu, da al'adunsu, har a lõkacin da Allah Ya bã shi rinjãye bayyananne a kansu, suka gãne amfãnin abin da yake kiran su zuwa gare shi na alheri, suka yãfe laifin da suke zato kuma suka so shi son da bã ya ƙãrewa har Tãshin Ƙiyãma. Wannan ni'imar Allah ce babba ga Annabinsa, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi. Hanya madaidaiciya, ita ce sharĩ'ar da Allah Ya bã shi, wadda ke jan jama'arsa a kan alheri har ya zuwa Tãshin ƙiyãma, kuma su tãshi a cikin alheri mafi girma, matuƙar dai sun bĩ ta, sun yi aiki da ita gwargwadon yadda ya nũna musu ita.

Fathu 48:10

[1] Asalin mubãya'a daga bai'u ne, watau ciniki, wanda ya yi mubãya'a ga Limãmin Musulmi kamar yã yi ciniki ne yã sayar da ransa, dõmin ya karɓi Aljanna daga Allah a Rãnar Ƙiyãma. Mubãya'a ta farko,ita ce wadda aka yi wa Annabi a Hudaibiyya wani ɗan gari ne kusa da Makka a hanyar Jidda, tafiyar kwana ɗaya. An ce tanã cikin Hurumi, waɗansu sun ce bã ta cikinsa.

Fathu 48:11

[1] Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, ya yi nufin tafiya Makka dõmin ya yi Umra sabõda mafarkin da ya yi cewa yã ga ya shiga Makka shi da Sahabbansa, sunã mãsu yin aski da saisaye na ibãda, sai ya ce wa ƙauyãwan da ke gefen Madina su fita tãre da shi dõmin kada Ƙuraishãwa su fãɗa shi da yãƙi,su tsare shi daga Ɗãkin. Kuma ya yi harama ya kõra hadaya dõmin mutãne su san bã yãƙi yake nufi ba. Sai waɗansu mãsu yawa daga ƙauyãwa suka yi nauyin fita, sukayi zamansu kuma suka ce: "Zai tafi zuwa ga mutãnen da suka yãƙe shi a tsakar gidansa a Madĩna, suka kashe Sahabbansa. Ba zã mu bĩ shi ba dõmin mu halaka kanmu.".

Fathu 48:15

[1] A bãyan sulhun Hudaibiyya Allah Ya yi wa Annabi alkawarin zai buɗe masa Haibara ya sãmi ganĩma mai yawa, amma kuma kada ya bari ƙauyãwan da aka nema su fita zuwa Makka, suka ƙi su fita tãre da shi.

Fathu 48:16

[1] Abũbakar zai kira su dõmin su yãƙi mutãnen Musailama, ko kuma su yãƙi Rũmu da fãrisa a bãyan rãyuwar Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Fathu 48:18

[1] A bãyan da Annabi ya sauka a Hudaibiyya, ya kirãyi Khuraish bn Umaiya el Khuzã'i ya aike shi Makka ya azã shi a kan rãƙuminsa dõmin ya gaya wa shugabanninsu cewa yãtaho Umra ne, bai zo da yãƙi ba. Sai suka sõke rãƙumin Annabi, kuma suka yi nufin kashe Khuraish amma Ahãbish suka hana su, ya zo ya gaya wa Annabi. Sa'an nan Annabi ya kira Umar bn Khattãb dõmin ya aika shi zuwa Makka, sai ya ce: "Ya Manzon Allah inã tsõron raina ga Ƙuraishãwa, bãbu banĩ Adiyyin bn Ka'ab a Makka balle su kare ni daga gare su, amma inã nũna maka wani mutum wanda ya fĩ ni dangi a cikinta shĩ ne Usman bn Affãn." Sai Annabi ya kira Usman ya aike shi zuwa ga Abi sufyãn da shugabannin Ƙuraish, ya bã su lãbãrin cewa bai zo yãƙi ba. ya taho ne dõmin ziyãra kawai ga wannan Ɗãki dõmin ya girmama alfarmarsa. Ya rubũta masa takarda ya tafi da ita. Kuma ya umurce shi da ya yi bushãra ga Musulmi mãsu rauni, cewa cin nasara yã yi kusa, kuma Allah zai ɗaukaka addininsa. Usman ya fita ya tafi Makka ya iske cewa Ƙuraishãwa sun haɗu a kan hana Annabi shiga Makka. Abban bn sa'ĩd bn Asi ya haɗu da Usman a lõklcin shigarsa Makka, sai ya ɗauke shi a kan rãƙumarsa, ya bã shi maƙwabtaka dõmin kada a kashe shi, har ya kai takardar Annabi. Suka nãce cewa Annabi bã zai shiga ba suka ce wa Usmãn: "Idan yanã son ɗawãfi sai ya yi," Sai ya ce bã zai yi ba sai Manzon Allah ya yi. Musulmi suka ce: "Usmãn ya ji daɗi yã yi ɗawafi," sai Annabi ya ce: "Ban yi zaton Usmãn zai yi ba." Sa'an nan lãbãri ya zo wa Annabi, cewa an kashe Usmãn sabõda haka Annabi ya ce: "Idan sun kashe shi, sai mun yaƙe su." Wannan ya sa aka yi masa mubãya'a a ƙarƙashin itãciyar ɗalh mai kama da farar ƙaya. A bãyan haka Annabi ya aza hannunSa na hagu a kan hannunsa na dãma, ya ce: "Gã hannun Usmãnu." Mãsu mubãya'a dubũ da ɗari uku kõ ɗari huɗu ne, da cewa za su yi yãƙi da Ƙuraishawa, bã zãsu gudu ba, sai dai su mutu. Daga nan shugabancin ya tabbata. Umar bn Khattãb yã sanya an sãre itãciyar nan dõmin mutãne sun fãra salla a ƙarƙashinta. Ba a yi yãƙi ba, sai aka yi sulhu. Annabi ya kõma a shekara mai zuwa yã yi Umra.

Fathu 48:20

[1] Cin nasara makusanci, shĩ ne cin Haibara, a bãyan kõmawar Annabi Madĩna a ƙarshen zul Hajji. Sa'an nan ya fita wajen ƙarshen Muharram shekara ta bakwai. Aka samo ganĩma mai yawa. Waɗansu ganĩmõmi na waɗansu ƙasãshen da zã a ci a nan gaba har ƙarshen dũniya. Ganĩmar Haibara ita ce aka gaggauta. [2] A lõkacin da Annabi ya fita daga Madĩna zuwa Hudaibiyya Allah Ya kange hannuwan Yahũdãwa daga iyãlan Musulmi na cikin Madĩna, in dã bã dõmin haka ba sai su je su fãɗa su da kashi da kãmu. Sai Allah Ya jefa tsõro a cikin zukãtansu.

Fathu 48:21

[1] Ganĩma da aka yi musu gaggãwa da ita, ita ce Haibara. Ganĩma wadda ba su da ĩko da ita, ita ce sauran ƙasãshen dũniya inda Musulmi suka ci, suka mallake shi, na ƙasar Rumãwa da farisãwa da Masar da sauransu.

Fathu 48:24

[1] Waɗansu Ƙuraishawa ne, sũ tamãnin, suka kewaye Musulmi a Hudaibiyya, da niyyar yaudara, sai aka kãme su, su duka, aka kai su ga Annabi, shi kuma ya yãfe musu, a bãyan ya nũna musu rinjãya. Wannan shĩ ne ya sabbaba yin sulhu.

Fathu 48:26

[1] A lõkacin da Ƙuraishi suka ga bã su iya yãƙi da Annabi, suka dõge da ƙabĩlancinsu, ta hanyar sulhu. Suka aika sahlu bn Amru da Huwaitib bn Abdul Uzza da Makraz bn Hafs bn Ahnaf dõmin neman sulhu bisa kada Annabi ya shiga Makka a wannan shekara, amma shekara mai kõmõwa ya je ya shiga Makka kwana uku, su kuma su fita har ya ƙãre Umra ya fita. Annabi ya karɓi sulhun. Aka ce Aliyu bn Abi Talib ya rubũta. Wajen rubũtun kuma aka so a yi tãshin hankali, dõmin ya rũbuta, Manzon Allah ya yi sulhu da Ƙuraishãwa, sai kuma suka ce ba su yarda a rubũta kalmar Manzon Allah ba. Sai Annabi ya sanya hannunsa mai daraja ya sõke kalmar da ake sãɓãni a kanta. Allah Ya saukar da natsuwa ga kõwa. [2] Kalmar taƙawa ita ce kalmar shahãda dõmin ɗaukar alkawari da ita yanã lazimtawa mai ita bin umurnin Allah da dãɗi kõ ba daɗi ta haka sai natsuwa ta sãmu. Anã ce mata kalmar taƙawa dõmin da ita ake kãre rai daga bin shaiɗan. Ma'anar taƙawa, ita ce kãriya.

Fathu 48:29

[1] Neman falala da sana'ar hannunsu, kõ fatauci, ba su zama nauyi a kan mutãne ba, kõwanensu ya dõgara ga Allah,sa'an nan yanã rãyuwa a kan hãlãliyarsa. [2] Kufan sujuda, shĩ ne hasken fuskõkinsu da annurinsu. fuska ita ce madũbin zũciya. Anã gãne zũciyar ƙwarai daga fuskarta. Bã ya halatta ga mutum ya riƙa darkãka gõshinsa ga ƙasã dõmin ya yi kwãdon salla. Wannan alãmar riya ce. Faɗakarwa. Nan ne ƙarshen dõgãyen sũrõri da ake cewa Muɗawwalãtu. An ƙãresu da sũrõri biyu, Ƙitãl dõmin yãƙi, da fat'h dõmin tsãrin gudãnar da siyãsa sabõda tsaron Addĩni. Bãyan haka kuma sai gajerun sũrõri, watau Mufassalãtu.

Hujurat 49:1

[1] Wannan yã nũna mana cewa bã yã halatta ga Musulmi ya yi wani aiki ko ya faɗi wata magana sai yã san hukuncin Allah a cikinsu. Kuma kada ya ƙãra wãyõnsa a kan abinda Allah Yã ce, kuma kada ya rage idan yanã da ĩkon cikãwa. Dukan wannan yakan ja Musulmi ga ɓãcin ayyukansa, watau ya yi ridda daga Musulunci.

Hujurat 49:2

[1] Ladubban zama da shugaba.Annabi shi ne kan shugabanni, sai dai ɗã'a gare shi wãjibi ne ga kõme, sauran shũgabanni kuwa ga abin da bai sãɓawa shari'a ba.

Hujurat 49:6

[1] Idan wani yã kai lãbãrin ɓarna, kada a yi aiki da shi sai bãyan an bincika an san gaskiyar al'amarin, kãfin a yi aiki da shi. fãsiƙi ga asalin kalma shi ne duka wanda ya karkace daga hanyar ƙwarai wadda aka sani. A nan, fãsiƙi, shi ne mai kai lãbãrin da yake akwai tãshin hankali a cikinsa, ko kuma abin tsõro dõmin ya sanya rũɗu a tsakãnin jama'a tun ba a san haƙĩƙanin al'amarin ba.

Hujurat 49:9

[1] Wannan tsãri na sulhu a tsãkanin al'umma biyu mãsu faɗa, shĩ ne hanya mafi kyau wadda har yanzu wayon dũniya bai kai ga yin aiki da shi ba. Dã yanzu an zauna lãfiya, dã Majalisar Ɗinkin Dũniya na iya aiki da shi. haka Yake kuma ga sauran hukunce-hukuncen mutãnen dũniya. Shari'ar Musulunci sabõda ãdalcin da ke cikinta kuma wayon dũniya bai kai ta ga anã iya zartar da shi ba, shĩ ne ya sa ƙasãshen Musulunci ke kaucewa gare ta, dõmin son ran shugabanninsu. Allah Yã mayar da mu ga addininmu! Dukan Musulmin da ya kaucewa sharĩ'ar Musulunci, to, ya kauce ne dõmin ya sami damar yin zãlunci, kuma idan yã halatta kaucewar, yã zama bã Musulmi ba.

Hujurat 49:13

[1] Yã kirãyi mãsu ĩmãni a cikin wannan sũra sau biyar ga abin da ya keɓanta da su na umurni da hani kamar yadda Lukmãn ya kirãyi ɗansa wajen yi masa wasiyyõyi. Kuma ya kirãyi mutãne a wannan ãyã ga abin da ya haɗa mũminai da kãfirai wajen halitta, watau alfahari da dangantaka. Dangantaka bã ta ɗaukaka wanda taƙawarsa ba ta ɗaukaka shi ba, kuma bã ta rage wanda taƙawarsa ta ɗaukaka shi. Fĩfĩkon taƙawa, shĩ ne fĩfĩko tabbatacce.

Ƙaf 50:12

[1] Rassi sunan wata rijĩya ce. Mutãnenta na zaune a gefenta da dabbõbinsu, sunã bauta wa gumãka, aka aika musu wani Annabi, anã ce da shi Hanzala bn safwan kõ kuma waninsa.

Ƙaf 50:14

[1] Ma'abũta ƙunci, mutãnen shu'aibu ne na farko. Bãyan an halaka su, sa'an nan ya tafi Madayana. [2] Tubba'u, sarkin Himyar ne,a Yemen, yã musulunta amma mutãnensa suka ƙi bin sa ga addini, aka halaka su, shi kuma ya tsĩra. Shĩ ne sarki wanda ya sãɓãwa ƙã'ida; ya musulunta amma mabiyansa ba su musulunta ba.

Ƙaf 50:23

[1] Malã'ika mai rubũtun aikinsa. Bã ya rabuwa da shi sai a hãlãye uku, wurin jimã'i da salga da wanka. Malã'ikan da aka haɗa shi da shi dõmin ya rubũta ayyukansa.

Ƙaf 50:27

[1] Shaiɗanin da ke tãre dashi. A cikin hadĩsi an ruwaito cewa kõwa yana da Shaiɗani tãre da shi, sai dai idan ya rinjãye shi, da abin da Allah Ya aza masa, ko kuma shi sai shaiɗãnin ya rinjãye shi da bin son zũciyarsa.

Ƙaf 50:30

[1] Wannan jawãbi na Jahannama yanã ɗaukar ma'anõni biyu. Ta farko tanã nũna ta cika ƙwarai, amma tanã kũkan a ƙara mata wani abu a cikinta. Wannan fassara ta yi daidai da ayãr da ta ce, "Lalle na cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya." Sura ta 32, ãyã ta 13. Fassara ta biyu, ita ce Jahannama nã neman ƙãri tanã hushi sabõda mãsu sãɓawa umurnin Allah. Sũra ta 67 ãyõyi 6, 7 da 8.

Ƙaf 50:33

[1] Tsoron Allah a fake, shĩ ne a bauta masa, bã da riya ba, ɓayyane da ɓõye duka ɗaya.

Ƙaf 50:34

[1] Kõ kuma ku shiga da sallama.

Ƙaf 50:36

[1] Sun nħmi wurin tsĩra, ba su sãmu ba, sabõda haka kãfiran yanzu ma ba su iya samun wurin tsĩra, sai dai idan sunkõma ga Allah ta hanyar Manzon Sa kawai, watau taƙawa ga Allah ke nan. Anã kãre azãbar Sa da ibãdar Sa kamar yadda Yake so.

Ƙaf 50:39

[1] Tasbĩhi game da gõdewa Allah a gabãnin fitar rãnã, shi ne sallar asuba, na gabãnin ɓacewarta, shi ne sallar Azahar da La'asar. Daga dare kuwa, shĩ ne sallar Magariba da Isha'i. Bãyan sujada, shĩ ne sallõli na nafila kuma ma'anarsa a nan tasbĩhi da tahmĩdi da kabbarõri a bãyan sallõli farillai talãtin da uku kõwace, sa'annan a cika ɗari da addu'ar da aka ruwaito a nan.

Ƙaf 50:41

[1] Mai kira shĩ ne Isrãfĩlu a cikin ƙaho a Baitil Maƙadis dõmin a nan ƙasa ta fi zama kusa da samã.

Ƙaf 50:45

[1] Wannan ya nũna ba a wa'azi da ilmin da bã daga Alƙur'ãni aka fitar da shi ba, sai fa idan bai sãɓawa abin da ke cikin Alƙur'ani ba.

Zariyat 51:57

[1] Bã Ni nufin su sãmo Mini abinci, kuma bã Ni nufin su dafa Mini abinci.

Tur 52:21

[1] Wannan ãyã tanã nũna yadda wani ke ceton wani sabõda kusanci dõmin a ƙãra daukaka mai ceton. Sharaɗin ceton shĩ ne wanda ake ceton yanã da nãsa ĩmanin. Wanda jinginarsa ta halaka bãbu mai cetonsa. Zuriya ta haɗa uwãye da almajiran mãlami sãlihi. Suna shiga a cikin cetonsa.

Tur 52:39

[1] Waɗansu Lãrãbawa sunãkiran Malã'ika 'ya'yan Allah mãtã, sunã kuma bauta musu dõmin su cece su daga Allah, suna yin gumãka da sũnansu.

Tur 52:48

[1] (Ma'anar ita ce tsarkakewa kõ tasbĩhi, 'tsare sallõli, farillai, anã cewa' faɗin "Subhãnal lãhi wal Hamdu Lillãhi" a bãyan kõwane mazauni, dõmin ya zama kaffãrar wannan mazaunin.

Najm 53:5

[1] Wahayin da ke zuwa ga Annabi bãbu ɓata a cikinsa dõmin Jibrilu mai kãwo shi ga Annabi, Malã'ika ne mai ƙarfi ƙwarai, wani Shaiɗãni bã ya iya taron sa dõmin ya musanya wahayin, kuma Annabi ya san shi sõsai, kuma idan ya kãwo wahayin, sai ya sauko kusa ƙwarai da Annabi, sa'an nan shi kuma Annabi ba rikitacce ba ne, yanã cikin hankalinsa.

Najm 53:13

[1] Lamirin Malã'ika Jibrila ne.

Najm 53:17

[1] Lamirin Malã'ika Jibrila ne.

Najm 53:18

[1] Watau dai Alƙur'ani ya zo daga Allah ta hanya mafi aminci har ya sadu da mutãne dõmin su yi aiki da abin da ke cikinsa.

Najm 53:19

[1] Watau kun bar Alƙur'ani kun kõma wa surkullen da kuke haɗãwa game da gumãka su Lãta da Uzza da Manãta. Kuna cewa sũ wakĩlan Mala'ikun da kuke bautã wa ne kuma su 'ya'yan Allah mãtã ne. Sunã cetonku daga Allah.

Najm 53:23

[1] Watau Alƙur'ani wanda Mala'ika jibrĩla ya zo wa Annabi da shi. Sun bar shi sun kõma wa tatsũniyõyi da gũrace-gũrace.

Najm 53:32

[1] Wanda yake mutumin kirki, Allah Ya san shi. Kada ku dinga tsarkake kanku da bãkunanku dõmin neman girma, kõ dõmin neman wani abu dabam.

Najm 53:49

[1] Sũnan wasu taurãri biyu ne sunã fita a bãyan taurarin Jauza'a sunã tafiya daga kudu zuwa arewa karkace. Kabĩlar Lãrabãwa ta Khuza'a na bauta musu da umurnin Abu Kabshah, ɗaya daga cikin kãkannin Annabi na wajen uwa dõmin haka ne Ƙuraishãwa ke ce wa Annabi Ibn abĩ Kabshah, wanda ya ƙãga sãbon addinĩn da ya sãɓawa na ubanninsa.

Najm 53:53

[1] Mutãnen Lũɗu da aka birkice ƙasarsu da su.

Najm 53:55

[1] Kamar abõkin magana kõ mai karãtu.

Najm 53:57

[1] Makusanciya ita ce Ƙiyãma.

Najm 53:59

[1] Al'ƙur'ãni.

Najm 53:62

[1] Anã yin sujadar karatu a nan, amma bã ta a cikin sujadai na tĩlas.

Ƙamar 54:1

[1] Ƙuraishãwa suka nemi Annabi ya yi addu'a dõmin wata ya tsãge wani ɓangaren nãsa ya fãɗo a ƙasã; ya yi addu'ar, watã ya tsãge, wani abu daga gare shi ya fãɗo kamar yadda suka nema.

Ƙamar 54:27

[1] Mutãnen Sãleh sun nemi mu'ujiza da rãƙuma, a fitar da ita daga dũtse, sai aka fitar da ita, kuma aka raba ruwan sha a tsakãninsu da ita.

Ƙamar 54:45

[1] Bushãra ce ga Annabi, cewa zai yi yãƙi da Kuraishi kuma zai rinjãye su. Sa'an nan yãkin ya auku a Badar.

Rahman 55:13

[1] Asalin lamiri "ku" yanã nũni ne ga nau'i biyu, watau mutãne da aljannu, sai dai bãbu lamirin abu biyu kawai a cikin Hausa, sai na jama'a. Jam'i a luggar Hausa ya fara daga biyu.

Rahman 55:26

[1] Yanã nufin ƙasa.

Rahman 55:31

[1] Mutãne da aljannu.

Waƙi'a 56:8

[1] Mazõwa dãma ko mãsu albarka waɗanda zã a baiwa takardunsu a dãma. Mazõwa hagu ko mãsu shu'umci waɗanda zã a baiwa takardunsu da hagu.

Waƙi'a 56:13

[1] Jama'a daga mutãnen farko, sũ ne Annabãwan farko da kaɗan daga cikin mutãnen ƙarshe, shi ne Annabi Muhammadu, sallallãhu alaihi wa sallama. Bã a shiga cikin wannan kashi da aiki sai dai da zãɓin Allah. Kuma an rufe ƙõfarsa. Bãbu sauran wani annabi wanda zai zo da wani addini sãbo a bãyan Annabi Muhammadu, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Waƙi'a 56:60

[1] Ãyã ta 60 haɗe take da ãya ta 61 watau, bã zã Mu kãsa musanya ku da waɗansu mutãne ba su tsaya matsayinku, sa'an nan kũ kuma Mu mayar da ku wata halitta.

Waƙi'a 56:87

[1] Idan kun kasance mãsu gaskiya ga da'awar rashin Tãshin Ƙiyãma, to, ku yi ƙõƙarin hana mutuwa ga mutãne dõmin ku hana cikar alkawarin tayarwa a bãyan mutuwa.

Waƙi'a 56:96

[1] A cikin rukũ'i anã tasbĩhi da cewa: "Subhãna Rabbiyal Azĩm wa Bihamdih." Ma'anarsa Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mai girma game da gõde Masa.

Hadid 57:8

[1] Wannan ya nũna bin umurnin Allah da nĩsantar abin haninSa shi ne bauta, dõmin Ya ambaci ciyar da dũkiya da yin jihãdi bauta ne.

Hadid 57:10

[1] Wannan ya nũna cewa sahabban Annabi sũ ne suka fi kõwane Musulmi a bãyansu daraja. Kuma akwai bambancin daraja a tsakãnin Sahabban farko da na bãya.

Hadid 57:16

[1] Wanda yayi ĩmani da Allah amma bai bi umurninSa ba, sai zũciyarsa ta ƙeƙashe,ĩmãni ya fita sa'an nan kuma ya zama fãsiƙi mai fita hanyar gaskiya. Barin ciyarwa da dukiya dõmin jihãdi yanã nũna ƙeƙashħwar zũciya daga ĩmãni, sabõda haka faɗa da zũciya dõmin tsaron ĩmãninta shi ne jihãdi mafi girma.

Hadid 57:17

[1] Mai rãyar da ƙasa a bãyan mutuwarta da ruwa. Yanã rãyar da zukãta sabõda tawãlu'i ga ambaton Allah da bin umumin Sa. Watau tawalu'i daidai yake da ruwa wajen rãyarwa ga matattu, sai dai kõwane da tãsa hanya.

Hadid 57:25

[1] Littafi a nan anã nufin dukkan Littattafan samã da aka bãyar a bãyan Nũhu da Ibrahĩm. Ma'auni kuma, shi ne sharĩ'ar da ke cikinsu. Baƙin ƙarfe kuwa dõmin kãyan aiki na amfãnin sana'õ'i da cũtar da ke a cikinsa na makãmai da kuma amfãnin tsaron addini da jihãdi. Littafi da ma'auni ana aiki da su wajen awon ibãdar Allah da mu'ãmalõli a tsakãnin mutãne.

Hadid 57:27

[1] Nũhu da Ibrahĩm da Annabãwan da ke bãyansu zuwa ga ĩsa ɗan Maryama. [2] Ruhubãnanci a Kiristanci kamar tasawwufi ne a Musulunci. Hana bidi'a yanã cikin jihãdi da tsaron addini bidi'a kuma kashe addini ne. Anã kashe bidi'a idan anã awon ayyuka da Littãfi kamar yanda ake hana zãlunci idan anã awo da sikeli kõ mũdu.

Hadid 57:28

[1] Manzon Allah a nan, shi ne Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Anã umarnin ma'abũta Littãfi da su bĩ shi dõmin su sãmi rabo ninki biyu. Mãsu ĩmani a nan su ne 'Ahlul Kitãbi' na ƙwarai.

Hadid 57:29

[1] Rashin saninsu ya hana su su bi Mahammadu ga sãmun falalar Allah; rabo biyu. Ga wata fassara, an ce harafin korewa ƙãri ne, watau ma'anarsa ita ce Allah Yã bãyar da rabo biyu ga waɗanda suka yi ĩmãni da Mazonsa, dõmin mutãnen littafi su san ba zã su iya hana abin da Allah Ya nufa ba.

Mujadala 58:1

[1] Wannan ƙissa tanã nũna cewa a Majalisar Annabi kõwa na da 'yancin shiga, namiji da mace, kuma ya faɗi abin da yake so, kõ da ya sãɓãwa abin da Annabi ya gani ƙãfin wani wahayi ya sauka. Gã wannan mace sunanta Khaulatu bnt Sa'alabah ta kai ƙãrar mijinta Ausu bn Samit wanda ya yi zihãri game da ita, watau ya ce idan ya kusance ta kamar ya kwãna da uwarsa ne. Ga al'adar lãrabãwa wannan bã saki bã ne, kuma ba ya iya kwana da ita har abada. Wannan shi ne takai ƙarã wurin Annabi har ta yi mahãwar da shi a kansa. Kuma wannan ƙissa tanã nũna gaskiyar Annabi, bai yi jawãbi ba ga abin da bai sãmi wahayi ba a kansa.

Mujadala 58:7

[1] A bãyan ƙissar zihãri, ya shiga maganar mãsu gãnãwa a cikin majalisa. Kuma ya nuna cewa ba a sifanta Annabi kõ a jingina wani abu zuwa gare shi sai idan abin nan yã fito daga Allah a cikin harshen Manzon Sa.

Mujadala 58:11

[1] Bãyan ƙissar hukuncin gãnãwa cikin majalisa, sai kuma hukuncin zaunãwa kõ tãshi dõmin wani ya zauna. Kuma ana fifita mãsu ilmi da zama ga wurin da ya fi dãcewa da su.

Mujadala 58:12

[1] Hukuncin tãyar da mutãne dõmin a gãna da Manzon Allah, bã ya halatta sai a kan larũra mai tsanani sabõda haka aka sanya gabãtar da sadaka, sa'an nan aka sõke shi da umurni da tsaron salla dõmin wa'azin da ke cikinta da kuma bayar da zakka.

Mujadala 58:14

[1] Bãyan maganar mãsu tãyar da mutãne dõmin gãnãwa a cikin majalisa, sai kuma munãfikai mãsu mu'ãmala da kãfirai, kuma su je su zauna cikin majalisar Musulmi dõmin su ɗauki rahõtonsu zuwa ga maƙiyansu.

Mujadala 58:22

[1] Waɗanda suka tsare dõkokin Allah, Allah zai ba su ƙarfin rai ga zartar da al'amuransu da kyau, kuma zai wadãta su a dũniya da Lãhira. Asalin rũhi shine rai. Anã nufin rãyuwar ĩmãni da ƙarfin halin fuskantar gaskiya.

Hashr 59:2

[1] Mazõwa Littãfi a nan, sũ ne Yahũdun Madĩna, watau Banĩ Nadĩr. [2] Kõrewa daga ƙasã, Annabi yã kõre su zuwa Haibara a gargaɗar farko, Umar ya kõre su daga Haibara zuwa Syria a gargaɗa ta biyu.

Hashr 59:7

[1] Ɗan hanya, shĩ ne matafiyin da guzuri ya ƙãre masa, yanã neman taimakon da zai mayar da shi garinsa.

Hashr 59:9

[1] Muhãjirĩna sun yi hijira zuwa Madĩna daga Makka kõ waɗansu wurãre. Ansar, su ne mutãnen Madĩna. Waɗannan sũ ne ya kamãta a yi mãmãkin yadda suka taimaki addini a lõkacin tsanani. Muhãjirina sun bar gidãjensu da dũyarsu sun yi hijira, Ansarai sun raba dũkiyarsu da gidãjensu da iyãlansu sun bai wa Muhãjirĩna dõmin taimakon addĩni.

Hashr 59:11

[1] Bãyan ya nũna yadda Allah ke taimakon mai binsa da taƙawa. Kuma yanã nũna yadda Yake tãɓar da mai binSa da munãfinci.

Hashr 59:15

[1] Kuraishãwa da aka kashe a Badar.

Hashr 59:18

[1] Daga wannan ãyã ta l8 zuwa ƙarshen sũra, yanã bayãnin hãsalin darasin sũrar ne dunƙule, da kuma ambatar muhimman abũbuwan da ta ƙunsa dõmin wa'azi da farkarwa ga mai hankali.

Mumtahana 60:1

[1] Wani Sahãbin Annabi da ake cewa Hãtibu bn Abi Balta'a, ya rubũta takarda zuwa ga Ƙuraishãwa yanã sanar da su cewa Annabi na zuwa garinsu da yãƙi, sai Allah Ya sanar da Annabi tun manzonsa bai isa ba ga Ƙuraishãwa, sai aka mayar da takardar. Da aka tambayi Hãtibu dalĩlin yin ta,sai ya ce dõmin yanã da ɗiya da dũkiya ne a can, dõmin haka ya so ya gaya musu zuwan Annabi kõ da yake yanã da cikakken ĩmãmin cewa Annabi gaskiya ne, kuma zai rinjãye su duk yadda aka yi. Sai Annabi ya karɓi uzurinsa, ba a yi masa kõme ba, sai dai abin da Allah Ya hana; kada Musulmi su sãke wata ma'amala da kãfirai a ɓõye, ko a bayyane sabõda dalĩlan da aka faɗa a cikin sũrar.

Mumtahana 60:3

[1] Ga wata ƙirã'ã zã a fassara wurin da cewa: za a rarrabe tsakãninku;.

Mumtahana 60:12

[1] A zãmanin jãhiliyya sun kashe 'ya'yansu mãtã ta hanya uku, ɗaya sabõda bãkance na addini, na biyu sabõda tsõron talauci; sunã turbuɗe 'ya'ya mãtã a bãyan sun shekara shida, na uku sabõda kunyar haihuwar mace, sai uwa ta yi rãmi, idan ta haifi namiji ta bar shi, idan kuma ta haifi mace, sai ta tũra ta a cikin rãmin ta turbuɗe. [2] Sunã tsintar yãro su mayar da shi ɗansu, haka kuma maza na yin tabanni, watau mutum ya mai da ɗan wani nãsa kamar yadda har yanzu kãfirai nã yin sa.

Mumtahana 60:13

[1] Allah Ya yi Fushi ga duk wanda ya sani kuma ya ƙi aiki da saninsa kamar Yahũdãwa da miyãgun Mãlamai. [2] Kãfirai ba su yarda da Tãshin Ƙiyãma ba, sabõda haka suke yanke ƙauna daga wanda ya mutu.

Jumu'a 62:2

[1] Lãrabawa sũ ne mabiya al'ãdu, watau ummiyyũn daga ummu, watau uwa watau kamar yadda uwãye suka haife su dõmin bã su da wani littãfi da suke bi sai al'ãdunsu da hukunce-hukuncen shaihunansu.

Jumu'a 62:3

[1] Su ne Ajamãwan da zã su musulunta su bi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Kõ kuwa duk wanda ya musulunta a bãyan sahabban Annabi. Wannan yanã nunã falalar sahabbai a kan waɗansunsu.

Jumu'a 62:5

[1] Tir da wanda ya yi siffa da irin siffõfin Yahũdu daga Musulmi wajen ɗaukar karãtun Alƙur'ãni amma kuma bai yi aiki da shi ba. Yahaya bn Yamãni ya ce: "Sunã rubuta nadĩsi bã su fahimtarsa, kuma bã su kula da ma' anarsa." Watau sunã wahala wajen ɗaukar ilmin da aka ɗõra musu ɗaukarsa amma kuma bã su yin amfãni da shi a wajen aikinsu da mu'ãmalõlinsu.

Jumu'a 62:6

[1] Ba a sãduwa da Allah sai a bãyan mutuwa. Masõyi nã bũrin sãduwa da masõyinsa, kuma bã zai yi gudun sababin sãduwar ba.

Jumu'a 62:9

[1] Ba a hana Musulmi aiki ba a kõwace rãna, sai dai an hana duk wanda Jumu'a ta lazimta a kansa da ya yi wani aiki wanda bã na tattalin salla ba a rãnar Jumma'a, a bãyan kiran salla. Anã nufi da kiran salla na biyu a bãyan limãmi ya zauna a kan mumbarinsa, dõmin wannan kiran aka sani azãmanin Annabi da Abubakar da Umar. Amma kira na farko, Usman bn Affãn ne ya fãra shi dõmin farkar da mutãne, a bãyan sun yi yawa kuma sun kama sana'õ'i. Kuma a bãyan an ƙãre salla, sai a wãtse zuwa ga ayyuka da neman abinci. Bã a tsayãwa yin wata nãfila a bãyan sallar Jumu'a, sai dai an so yin raka'a biyu a bãyan fita daga masallãci kamar yadda Annabi ke yi. A farko, anã yin huɗubar sallar Jumma'a a bãyan salla har a lõkacin da ãyarin Dihyatul Kalbi ya kõmo daga shãm (Syria) da abinci,ya sauka a Baƙĩ'a, suka buga ganga, sai Sahabbai suka fita dõmin neman sayen abincin a gabãnin a ƙãre huɗubar suka bar mutum gõma shã biyu tãre da Annabi. Sai aka mayar da huɗubar a gabãnin salla. Kuma an fahimci cewa anã yin huɗuba a tsaye. Kuma ba a kafa Jumu'a, sai a kafaffen gari, amma Jumu'a nã ƙulluwa da mutum gõma sha biyu da lĩman.

Munafiƙun 63:1

[1] Munãfuki, a zãmanin Annabi, shine wanda ya bayyana Musulunci, amma kuma a ɓõye Shĩ kãfiri ne. A bãyan Annabi anã cewa munãfuki zindĩƙi.

Munafiƙun 63:4

[1] Munãfukai sunã da kyawun sũrar jiki kuma sun iya magana da fasaha amma fa bã su da hankali sabõda ƙaryar da suke a kanta, sabõda haka sunã tsõron kõwane irin mõtsi ya zama a kansu.

Munafiƙun 63:8

[1] Abdullah bn Ubayyi bn Salũl ya faɗi cewa "Wallahi idan mun kõma Madĩna wanda ya fi ƙarfi, lalle zai fitar da wanda ya fi ƙasƙanci." Yanã nufin Ansãrai mutãnen Madĩna zã su kõri Muhãjirai. Yã faɗi haka a cikin wata tafiya ta jihãdi. Aka gaya wa Annabi, sai ya yi musu. Allah Ya kunyata shi.

Tagabun 64:14

[1] Maƙiyi, shĩ ne mai hana mutumin da yake ƙiyayya da shi wani alheri ya sadu da shi. Idan son dũkiya kõ mãta kõ ɗiya ya hana mutum yin sadaka kõ fita zuwa jihãdji, to dũkiyar da mãtan da ɗiyan sun zama maƙiyansa ke nan.

Tagabun 64:15

[1] Fitina, ita ce duk abin da zai cũci mutum ta hanyar da yake amincewa, cũtar ta dũniya ce kõ ta Lãhira. Cũtar Lãhira ta fi tsanani sabõda girman hasãrar da ke a cikinta.

Talaƙ 65:1

[1] Saki, shĩ ne warware ƙullin halaccin sãduwa da jũna a tsakãnin miji da mãta. Haƙƙi ne wanda Allah Ya saka ga hannayen maza ban da mãtã. saki ga idda, watau ya sake ta saki gudã a cikin tsarkin dabai shãfe ta ba dõmin sauƙin idda. Yanã haramta ga mijin da mãtar ya fitar da ita kõ ta fita daga ɗãkinta a lõkacin idda. fãruwar wani al'amari shi ne sõyayya a bãyan ƙiyayya da mayarwa a bãyan saki. Alfãsha a nan, tanã nufin faɗa da zãge-zãge a kan surukantã. Anã fitar da mai iddar saki sabõda alfãsha daga gidanta.Akwai saki na sunna kuma akwai na bidi'a, amma saki na sunna ɗaya ne, a cikin tsarkin da bã a shãfe ta ba kuma kada a ƙãra mata wani saki har ta ƙãre idda, sakin bidi'a kuwa shĩne uku gabã ɗaya kõ a cikin idda gudã, a cikin haila kõ jinin bĩƙi. Sakin bidi'a yanã 1azimta, Anã tĩlastã shi mayarwa ga wadda aka saki a cikin haila idan bai kai uku ba ga miji 'yantacce, kõ biyu ga miji bãwã.

Talaƙ 65:4

[1] Muddar idda ga wadda ta yanke ɗammãnin haila, sabõda tsũfa, watanni uku,kuma bã zã ta ƙãra kõme ba a kai. Wadda take akwai shakka a game da ita ga kõ akwai ciki kõ bãbu shi, to, zã ta yi iddar wattani uku kuma ta yi jiran watanni tara, watau ta yi watannin shekara, uku na idda, saurãn na fidda shakkãne. Haka ne hukuncin mai istihãla, watau jinin ciwo. Amma yãrinya mai shakkar ciki, sai ta zauna har shakka ta gushe. Yarinyar da ba ta fãra haila ba tana iddar wata uku. Bãbu bambanci a tsakãnin ɗiya da baiwa ga idda da watanni, amma ga idda ta tsarki, to, baiwã tana yin rabin na ɗiya ga saki da mutuwa.

Talaƙ 65:6

[1] Mijin zai fita ya bar wa mãtar da ya saki ɗaki ta zauna a ɗakinta har ta ƙãre idda. Anã ciyar da mai sakin kõme, amma bã a ciyar da mai sakin bã'ini sai idan tanã da ciki. Ijãrar shãyarwa tanã akan uba ga uwar da aka saki saki bã'ini kõ ga watarta, bisa ga yardar sassan biyu.

Talaƙ 65:8

[1] A bãyan da ya gama bayãnin saki da hukunce-hukuncen da suka rãtayu a gare shi, sai kuma ya gõya gargaɗi ga wanda bai bi waɗannan hukunce-hukuncen ba, ta hanyar tsoratar da shi da cewa Allah Ya halaka alƙaryu mãsu yawa sabõda sãɓã Masa ga hukunce-hukuncen Sa ga ƙanãnan abũbuwa, balle mutum guda wanda ya sãɓã masa ga babban al'amari kamar aure da saki waɗanda rãyuwar ɗan Adam ta dõgara a kansu kuma ya yi bushãra ga wanda ya bĩ shi da taƙawa, ya fita daga duhun al'ãdu zuwa ga hasken sharĩ'ar Sa, kuma Ya yi wa'adi da bã shi sauƙin rãyuwa daga wadãtar Sa mai yawa.

Talaƙ 65:11

[1] Allah Yã kyautata wa wanda ya tsare sharĩ'arsa da kyau, awajen arzikinsa tun daga dũniya har ya zuwa Lãhira, dõmin Yã ce: "Haƙĩƙa Allah Yã kyautatã masa (mai tsare sharĩ'ar) arziki," bã da Yã yi ƙaidin lõkaci kõ wuri ba.

Tahrim 66:1

[1] A cikin littãfin Buhãri an ruwaito daga A'isha, mãtar Annabi, cewa Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gareshi, yakan yi jinkiri a wajen Zainab bint Jahsh dõmin ya shã zuma a wurinta. Ta ce: "Sai na shirya, nĩ da Hafsah: Duk wadda Manzon Allah ya shiga gurinta daga garemu, ta ce masa, 'Ina jin wãrin tsimi daga gareka! Kã ci tsimi! To, sai Annabi ya shiga ga ɗayansu, ta ce masa: "Kã ci tsimi." Ya ce: "A'isha! Nã shã zuma dai a wurin Zainab bint Jahsh, kuma ba zan kõma gareshi ba." Asalin abin, Annabi tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi,yã kasance yanã zagayãwa a gidãjen mãtansa a bãyan sallar la'asar dõmin ya gaishe su. To, sai ya sh ga ga Hafsah bãyan ya shiga ga Zainab, ta gaya masa haka. Kuma ya gaya mata nĩsantarsa ga zuma, kuma ya gaya mata lãbãrin cewa Abubakar da Umar, Allah Ya yarda da su, za su zama halĩfai a bãyansa. To, sai ta faɗi waɗannan lãbãru ga maƙwabciyarta A'isha. Wannan Ƙissa tana koyar da sauƙin halin Annabi a game da iyãlansa, da girmamawarsa a gare su.

Tahrim 66:2

[1] An rubũta yadda ake warware rantsuwa da kaffãra wadda aka ambata a cikin sũra ta 5, ãyã ta 89. Anã kaffãrar rantsuwa da ciyar da miskĩnai gõma daga matsakaicin abinci, mũdu biyu ga kõwane, kõ tufãtar da su tufar da za ta ishe su salla, idan bai sãmu ba, ya yi azumin kwãna uku.

Tahrim 66:6

[1] Tsare kai da iyãli daga wuta yanã sãmuwa da shiryar da su da karãtu da nasiha a kan addini. Wannan yanã a cikin kyawun zamantakewa wanda sũrar ke karantarwa.

Tahrim 66:7

[1] Kãfirai a nan, kafircinsu sabõda ƙin bin umurnin Allah game da kyawun zamantakewa da iyali yake. Laifinsu yã fi sauran laifuffuka dõmin yanã sabbaba yãmutsi a gida, har abin ya shãfi zurriya da ƙasã gabã ɗaya.

Tahrim 66:8

[1] Allah Yã yi alkawarin bã zai kunyatar da AnnabinSa ba, haka kuma waɗanda sukayi ĩmãni tãre da shi, watau sahabbansa a Rãnar Kiyãma. Wannan shĩ ne dalĩlin da ya sa Allah Ya tsare Annabi da Sahabbansa daga bauta musu kamar yadda aka bautã wa waɗansu Annabãwa da Sãlihai waɗanda Allah zai tambaye su kõ sũ ne suka yi umurni da a yi musu bautar, sũ kuma su faɗi barrantarsu daga waɗanda suka bauta musu.

Tahrim 66:10

[1] Waɗannan misãlai biyu,mãtar Nũhu da mãtar Lũɗu sunã nũna kusanci ga sãlihai bã ya isa ga addini sai kõwa ya yi abin da Allah Ya yi umurni da shi. Kuma anã kallafa wa mãtã da su kiyãye kyawun zamantakewa da mazansu. Kuma anã yi musu azãba sabõda sãɓa wa Allah ga barin haka kamar yadda ake ga mazansu.

Tahrim 66:11

[1] Wannan yanã nũna cewa kusantar kãfiri bã zai cũci mũminai ba. Sai dai Allah Yã hana aure a tsakãnin Musulma da kãfiri.

Tahrim 66:12

[1] Wannan yanã nũna cewa rashin aure ga mãtar da ke iya tsare farjinta daga alfãsha kuma ta tsare addininta da taƙawa, bã zai cũce ta ba ga sãmun rahamar Allah a dũniya da lãhira.

Mulk 67:30

[1] Ana so idan mai karatu ya kai ƙarshen wannan sũra ya ce: الله رب العالمين wato Allah Ubagijin halitta. An karanta wannan ãya a gaban wani kãfiri, sai ya ce zã mu fito da ruwan game da amfãni da dundurũsai da farħtani, sai ruwan idãnunsa ya faƙe.

Ƙalam 68:33

[1] Irin wannan azãba ce za a yi wa Ƙuraishãwa, dangin Annabi, kamar yadda aka yi wa mãsu gonar lambu, wãto da suka tũba aka musanya musu da abin da ya fi abin da suka sãba sãmu. Wato an gayã wa Annabi ne lõkacin da danginsa suka kangare, suka ƙi shiga Musulunci, aka yi musu azãbar fari, da rashin ruwa shekara bakwai, Allah Ya gaya masa cewa, zã su musulunta, alheri ya kõma musu. Ya kuwa kõma, kamar yadda Allah Ya yi alkawari

Jinn 72:16

[1] Tsayuwa sosai wato su bautawa Allah kamar yadda Allah Ya umarce su, su yi Masa ɗa'a saboda Yã wadãta su.

Jinn 72:19

[1] Bawan Allah shi ne duk wani mai wa'azi yana kira zuwa ga Allah. Bã ya halatta a gare shi ya bar waɗanda yake yi wa wa'azi su kai fagen bauta Masa shi kansa. Sai ya gaya musu gaskiyar matsayinsa, kamar yadda Allah Ya faɗa wa AnnabinSa, kuma Ya umarce shi da ya gaya wa waɗanda yake yi wa wa'azi.

Jinn 72:27

[1] ldan Allah Yã aiko wani manzonsa da wani umurni ko hani zuwa ga mutãne to zai sanya mala'iku gaba gare shi da bãya gare shi suna gãdin sa dõmin kada wani Shaiɗãni ya kusance shi har ya sanya shi mantuwa ko kuskure, har ya iyar da manzancin nan kamar yadda yake.

Muzzammil 73:15

[1] Wato Annabi Muhammad, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi. [2] Wato Annabi Mũsã, aminci ya tabbata a gare shi.

Ƙiyama 75:1

[1] Wasu na fassarawa: lna rantsuwa da Rãnar Ƙiyama. A ganina, da tabbatar da rantsuwar da kuma kore ta duka ɗaya ne, maƙasũdi dai jan hankalin mai karãtu ga abin da yake a ciki, na hikimar Allah.

Ƙiyama 75:2

[1] Kowane rai na zargin kansa idan bai yi aikin alheri ba, ko kuma bai yi fiye da wanda ya yi ba, ko kuma bai aikata wanda ya fi kyãwo ba a lokacin aikinsa.

Ƙiyama 75:16

[1] Dangantakar wannan ãya da ta sama da ita, ita ce bambancin Annabi mai gaggawar karɓar umurnin Allah da ƙyamar kãfiri ga karɓarsa, da bayãnin sauƙaƙewar Allah ga mai bin umurninSa.

Ƙiyama 75:30

[1] Ranar kora mutane, kamar ana gargaɗa tumãki, zuwa ga tsayuwa a gaba ga Allah, dõmin hisabi.

Ƙiyama 75:40

[1] Ana son mai karãtu a nan ya ce: a ɓoye بلى وأنا على ذلك من الشاهدين.

Insan 76:13

[1] Kishingiɗa.

Mursalat 77:4

[1] Yã kamanta Manzanin Allah masu kãwo ayõyinsa da iskõki mãsu kãwo ruwa dõmin rahamar da ke cikin kowannensu.

Mursalat 77:13

[1] Yin hukunci a tsakanin tãlikai.

Nazi'at 79:20

[1] Ãyar Mũsã da ta fi girma ita ce sandarsa mai zama maciji ko hannunsa mai haske kamar tõcila idan yã sanya cikin hammata yã fitar.

Abasa 80:1

[1] Wani makãho, Abdullahi bin Ummi Maktũm ya je wurin Annabi dõmin ya musulunta, sai ya iske a lõkacin nan Annabi na ƙõƙarin shiryar da wasu manyan mutãne na Ƙuraishãwa, sai wannan makãhon ya yanke maganar Annabi da su, bã da saninsa ba, alhãli Annabi na bũrin su musulunta dõmin darajarsu ga idon mutãnensu. Saboda haka Annabi, (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), ya ɓata Fuska, ya tafi dõmin ɓacin ransa, saboda rashin musuluntarsu. Bãyan haka Annabi nã girmama Abdullahi ƙwarai, idan ya je wurinsa sai ya ce masa "Maraba da wanda Ubangijina Ya zarge ni sabõda shi." Kuma ya shimfiɗa masa mayafinsa, idan ya fita tafiya, yakan sanya shi riƙon garin Madina, ƙissar tana nũna girmamawar Allah ga Annabi da Ya ce: "Ya game Fuska." Bai ce masa: "Domin ka game Fuska" ba, sai ya faɗa a cikin hali mai sauƙi.".

Takwir 81:4

[1] Rãƙuma mãsu ciki ɗan wata gõma.

Takwir 81:7

[1] Ko kuma, aka haɗa kõwane mutum da irin mutãnensa a Aljanna ko a wuta.

Takwir 81:8

[1] A cikin zãmanin jahiliyya Lãrabãwa bã su son a haifa musu 'ya'ya mãta dõmin haka har sukan turbuɗe 'ya'yansu dõmin kada su yi abin kunya ko kuma su talauce wajen yi musu aure.

Takwir 81:15

[1] Masu tafiya suna kõmawa bãya.

Takwir 81:23

[1] Annabi ya ga Mala'ika Jibirilu ya san shi. Sabõda haka wani aljani bã zai yi kama da shi ba balle ya kãwo masa ƙarya.

Takwir 81:24

[1] Ma'anar gaibi a nan, ilmin da Allah Ya aiko Jibirilu da shi zuwa ga Annabi Annabi ba ya ɓõye shi daga mutãne. Ga wata ƙira'a, wanda ake tuhuma, wãto ba a tuhumar Annabi, ga gaibin da ya faɗi cewa daga Allah yake, wato Alƙur'ãni duka gaskiya ne.

Mutaffifin 83:3

[1] Mũdu.

Mutaffifin 83:21

[1] Malã'iku masu daraja.

Mutaffifin 83:36

[1] Amsar tambaya "na'am.".

Buruj 85:2

[1] Rãnar Ƙiyãma.

Buruj 85:3

[1] Rãnar Arafa.

Buruj 85:4

[1] Mutãnen Najiran ne suka yi rãmi suka hũra wuta a ciki, dõmin su ƙõne wanda yã yi ĩmãni da addinin Masĩh Ĩsa dõmin su hana yãɗuwarsa. Suka umurci kõwane Musulmi ya jefa kansa a ciki, su kuma suna zazzaune suna kallo.

Tariƙ 86:3

[1] Wannan ya yi kama da zuwan Annabi a cikin jahiliyya don ya haskaka duniya da ilimi kamar yadda girgije ke ba da ruwa saboda tsiron ƙasa, hantsar uwa ta ba da nono saboda jariri kuma maniyi ya zo lokacin Jima'i.

Tariƙ 86:12

[1] Dõmin fitar tsiro.

Tariƙ 86:13

[1] Mai rabewa tsakanin ƙarya da gaskiya.

Tariƙ 86:14

[1] Kãkãci.

A'ala 87:15

[1] Ya ambaci sũnan Allah ga ayyukansa duka, ya yi sallolin nan biyar da sauran.

A'ala 87:16

[1] Rayuwa iri biyu ce, ta dũniya da ta Lãhira.

A'ala 87:18

[1] Kamanta rãyuwar ciyãwa da rãyar da ummiyyi da ilmi bãbu mantuwa, da rãyar da mãtattu cikin sa'ãda ko cikin shaƙãwa yana cikin litaffan farko.

Gashiya 88:15

[1] Matãsan kai.

Fajr 89:7

[1] Tsawo mai ma'ana.

Fajr 89:9

[1] Wãdil-ƙura, sunan wuri ne kusa da Madina wajen Syria, wato Sham.

Balad 90:1

[1] Allah Ya ce ba sai Ya yi rantsuwa da Makka ba, sa'an nan zã a san darajarta a lõkacinda Annabi yake a cikinta, kuma shi yana da haƙƙin zama a cikinta mahaifansa da zurriyarsa duka, ko da yake zai yi hijira sabõda fitinar kãfirai mãsu halaka dũkiyarsu kan adãwa da shi. Dã sun yi amfãni da dukiyar ga ayyukan alheri, dã yã fi musu.

Balad 90:6

[1] Nã halaka dukiya mai yawa dõmin faɗã da addĩni.

Balad 90:10

[1] Hanyar alheri da ta sharri.

Balad 90:18

[1] Ko kuwa waɗanda ake bai wa takardunsu da dãma, a Lãhira.

Balad 90:19

[1] Ko kuwa waɗanda ake bai wa takardunsu da hagu, a Lãhira.

Shams 91:9

[1] Karɓar imãni da aiki da abinda ya ƙunsa tsarkake rai ne.

Shams 91:10

[1] Kãfirci turbuɗe rai ne da zunubi.

Laili 92:6

[1] Kalma mai kyãwo ita ce Kalmar shahãda da abin da ta ƙunsa na addinin Musulunci, wanda yake yinsa kamar yadda Allah Ya ce, ta hanyan Manzon Sa, shi ne taƙawa.

Laili 92:17

[1] Mafi taƙawa da Mafi shaƙãwa suna ma'anar mai taƙawa da shaƙiyyi.

Duha 93:4

[1] Ta ƙarshe, wãto, Lãhira; kuma ta farko, wato, dũniya.

Tini 95:1

[1] Ibn Abbas ya ce: 'Attinu shi ne masallacin Nuhu a kan Judiyyi, Azzaitun Masallacin Baitil Muƙaddas.'.

Tini 95:2

[1] Dutsen da Allah Ya yi magana da Musa a kansa. Ma'anarsa dutse mai albarka sabõda itacen da ke kansa.

Tini 95:3

[1] Gari amintacce shi ne Makkah.

Tini 95:8

[1] Ana son wanda ya karanta sũrar har ƙarshe ya ce بلى ,wato na'am, Allah Ya fi kowa kyãwon hukunci.

Alaƙ 96:19

[1] Wato salla da sauran ibãdu.

Bayyina 98:2

[1] Shi ne Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, dõmin bãbu wanda ya dãce da abin da ke cikin littafansu sai shi.

Asr 103:1

[1] Wasu suna fassarawa da lokacin sallar La'asar da kuma marece. A kõwane dai, an bai wa lokaci muhimmanci, zãmani yana yanke wanda bai yanke shi ba. ba ya halatta ga mutum wata mudda ta zãmani ta wuce shi bai san amfãnin da ya sãma wa kansa a cikinta ba, kuma kõme ya sãmu idan ba addini ba ne, to, hasãrace.

Fil 105:1

[1] An yi Yãƙin Gĩwa shekarar haihuwar Annabi tsakãnin halaka su da haihuwarsa kwãna hamsin. Bayan shekara arba'in Annabi ya fara karantar da mutane. Ya karantar da su cikin shekara ashirin da uku, sa'an nan ya ƙaura. Bayansa da shekara hamsin waanda suka bi shi suka cinye duniya. Wannan yana nuna cewa mutane ba su samun daraja sai da riƙon addini da ilimi.

Kafirun 109:5

[1] Ãya ta 4 da ta 5 sun nũna addinin ƙarya yakan canza amma na gaskiya bã ya canzawa.

Masad 111:4

[1] Anã fassara shi da mai tsegumi, wãtau annamĩmanci; da Lãrabci anã ce wã mai annamĩmanci "mai ɗaukar itacen wuta.".

Nas 114:4

[1] Shaiɗan yakan ɓõye idan ya ji an ambaci sunan Allah, dõmin haka aka yi masa suna mai ɓõyewa, wãto bã ya zuwa wurin da ake karatu da wa'azi, kamar yadda bã ya zama cikin zũciyar mutum mai ibãda da gaskiya. Ibãda ta gaskiya ita ce wadda aka yi ta kamar yadda Allah Ya ce a yi ta. Banda ibãdar bidi'a, ba ta korar Shaiɗan. Kuma da sharaɗin a yi ibãdar da kyakkyawar niyya, dõmin aikin da bãbu niyya mai kyãwu game da shi ɓãtacce ne.